September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar dokokin Jihar Kano ta yanke hukuncin dandatsa akan masu fyade.

2 min read

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara duba yiwuwar sauya dokokin hukunta masu fyade a jihar domin tsaurara su, ta yadda idan zai yiwu a riƙa fiɗiye masu irin wannan laifi.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Rano, Hon. Nuradeen Alhassan ne ya gabatar da kudurin, inda ya nemi abokan aikinsa su amince da hukuncin ‘fidiya’ a kan duk wanda kotu ta samu da laifin a nan gaba.

Ya shaida wa BBC cewa tun da dokar da ake da ita a yanzu ba ta sauya komai ba, lokaci ya yi da za a sauya ta, duba da yadda al’ummar Kano suka nuna bukatar hakan.

”Mutane gani suke kamar abin wasa ne, domin idan ana zargin mutum da fyade sai ka ga kafin ma a kai shi kotu, zai dauko lauyansa, karshe ma abin ya zama shiririta” In ji shi.Bisa dokokin da ake da su a yanzu a jihar Kano, idan kotu ta kama mutum da aikata fyade zai iya fuskantar daurin shekara goma sha hudu a gidan yari.

Sai dai yan majalisar na cewa wannan bai wadatar ba, mai yiwuwa ma shi yasa ake samun karuwar matsalar har kawo wannan lokaci.

A baya-bayan nan dai hankulan al’ummar Najeriya sun yi matuƙar tashi sakamakon ƙaruwar ayyukan fyaɗen da ake samu.

Fyade bai tsaya a kan manya ba ko ‘yan mata ba, galibi a wannan zamanin an fi cin zarafin kananan yara da jarirai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *