July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Matar da ta dawo daga rakiyar ‘yan IS ta yi nasara a Kotun Ɗaukaka Ƙara

2 min read

Alkalai a London sun yanke hukunci cewa Shamima Begum, wadda ta bar Burtaniya a lokacin tana ‘yar makaranta ta je ta mara wa ‘yan kungiyar IS baya a Syria, za ta iya komawa ta kalubalanci gwamnati a kan matakin soke kasancewarta ‘yar asalin Burtaniya.

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce ba a ba ta damar gabatar da korafinta daga sansanin da take a arewacin Syria ba inda ake tsare da ita a can.

Shamima mai shekara 20 a yanzu, na daya daga cikin ‘yan mata ‘yan makaranta uku da suka bar Landan don shiga kungiyar IS a shekarar 2015.

Tun tana shekara 15 ta yi wasu abubuwa na fitina wadanda taga baya aka zo aka kamata da laifin aikata su.

Yanzu haka dai ta yi aure inda ta auri wani dan IS din har suka samu ‘ya’ya uku wadanda dukkan su a yanzu sun mutu. Tuni dai gwamnatin Burtaniya ta yi Allah-wadai da hukuncin kotun inda ta bukaci damar daukaka kara.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar ce ta kwace shaidar zamanta ‘yar Burtaniya kan hujjojin tsaro bayan da aka gano ta a wani sansani a 2019.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce an ki sauraron kararta ne sanoda ba ta iya gabatar da hujjoji daga sansaninta na Syria ba.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ce hukuncin kotun bai yi mata dadi ba kuma za ta daukaka kara.Hukuncin na nufin dole a yanzu gwamnati ta samo hanyar barin matashiyar, wacce a yanzu take Sansanin Roj a arewacin Syria, ta bayyana a gaban kotu a Landan duk da ta sha maimaita cewa ba za ta taimaka wajen fitar da ita daga Syria ba.

Masu Shari’a Lord Justice Flaux da Justice King da kuma Lord Justice Singh – sun ce: “Dole a yi adalci a kan lamarin nan wajen ganin rinjayi fargabar samar da tsaro ta hanyar ba ta damar shiga kasar don ta bayyana a gaban kotu.

Mai shari’ar ya kuma ce za a warware matsalar damuwar da ake da ita a kan tsaron idan har ta koma Burtaniyan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *