June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Real Madrid ta lashe La Liga na bana kuma na 34 Jumulla

3 min read

vReal Madrid ta lashe kofin La Liga a karon farko tun bayan shekara uku, bayan da ta doke Villareal 2-1 a wasan mako na 37 da suka fafata ranar Alhamis a filin wasa na Alfredo Di Stefano.

Karim Benzema ne ya fara ci wa Madrid kwalon farko ta tsakanin kafar golan Villareal, Sergio Asenjo, sannanya ci na biyu a bugun fenariti da ya buga sau biyu, bayan takaddama.

Vicente Iborra ne ya zare daya amma hakan bai girgiza Madrid ba, wacce ta lashe kofin La Liga na bana kuma na 34 jumulla.

Kungiyar da Zinedine Zidane ke jan ragama ta ci dukkan karawa 10 da ta buga, tun bayan da aka ci gaba da wasannin shekarar nan.

Madrid za ta buga wasan mako na karshe na 38 a mataki na daya da tazarar maki bakwai tsakani nta da Barcelona wacce Osasuna ta doke ta 2-1 a Camp Nou.

Arsenal ta yi wa Liverpool fancalen hada maki 100 a Premier
Liverpool za ta daga kofin Premier bayan karawa da Chelsea
Madrid wacce ta lashe dukkan karawar da ta buga, bayan da aka ci gaba da La Liga ta yi wasa 37 jumulla kawo yanzu.

Daga ciki ta yi nasara a guda 26 da canjaras 8 aka doke ta fafatawa uku ta kuma ci kwalloi 68 aka zura mata 23 a kakar bana.

Cikin watan Maris aka dakatar da wasannin La Liga don gudun yada cutar korona.

”Yan wasan Real Madrid da koci Zinedine Zidane ya fuskanci Villareal a filin wasa na Alfredo Di Stéfano.

Wadan da za su buga karawa da Villareal:

Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Militão da Ramos da Varane da Nacho da kuma Mendy.

Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Isco.

Masu cin kwallo: Hazard da Benzema da Bale da Lucas Vázquez da Jović da Asensio da Brahim da Mariano da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.

Sakamakon wasannin mako na 37 a gasar La Liga ranar Alhamis.

Eibar 3-1 Real Valladolid
Athletic Bilbao 0-2 Leganes
Barcelona 1-2 Osasuna
Real Betis 1-2 Deportivo Alaves
Celta Vigo 2-3 Levante
Real Mallorca 1-2 Granada
Real Madrid da Villarreal C
Real Sociedad 0-0 Sevilla
Valencia 1-0 Espanyol
Getafe 0-2 Atletico Madrid
Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar bana:

Lionel Messi Barcelona 23
Karim Benzema Real Madrid 21
Gerard Moreno Villarreal 16
Raul Garcia Athletic Bilbao 16
Luis Suarez Barcelona 15
Lucas Ocampos Sevilla 14
Iago Aspas Celta de Vigo 14
Alvaro Morata Atletico de Madrid 12
Ante Budimir Real Mallorca 12
Roger Marti Levante 11
Willian Jose Real Sociedad 11
Santi Cazorla Villarreal 11
Lucas Perez Deportivo Alaves 11
Jaime Mata Getafe 11
Wasannin mako na 38 da za a buga ranar 19 ga watan Yuli:

Deportivo Alaves da Barcelona
Atletico Madrid da Real Sociedad
Espanyolda Celta Vigo
Osasunada Real Mallorca
Sevilla da Valencia C.F
Real Valladolid da Real Betis
Villarreal da Eibar
Leganesda Real Madrid CF
Levante da Getafe CF
Granada da Athletic Bilbao
Jerin kungiyoyin da suka lashe La Liga:

Real Madrid 34
Barcelona 26
Atletico Madrid 10
Athletic Bilbao 8
Valencia 6
Real Sociedad 2
Deportivo La Coruna 1
Sevilla FC 1
Real Betis 1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *