Shugaban Nigeria Buhari ya ce zai binciki kudaden Naija.
1 min read
hugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya sha alwashin gano matsalar da ke durkusar da ci gaban yankin Neja-Delta a kudu maso kudancin kasar, duk da irin dumbin dukiyar kasa da ake sadaukarwa yankin duk shekara.
Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na tuwita a ranar Alhamis da yamma, inda ya kara da cewa ”wannan gwamnatin a shirye take wajen kawo ci gaba cikin gaggawa kuma mai dorewa a yankin.”
Wannan batu na shugaban na zuwa ne a ranar da wasu jami’an tsaro suka zagaye gidan Joy Nunieh – tsohuwar shugabar Hukumar Raya Yankin Neja Delta NDDC, tare da ƙoƙarin kutsawa gidan nata don kama ta, kan wasu zarge-zarge.
Duk da cewa Shugaba Buhari bai ambaci batun Nunieh ba, amma a sakon nasa ya ce ya fayyace wa Majalisar Dokoki da hukumomin bincike da na tsaro cewa su yi kokarin yin aiki tare da juna, domin a samu damar tabbatarwa da kuma cimma gaskiya da yin ƙe-ƙe da ƙe-ƙe a harkar arzikin ƙasa.