June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ɗaliban Najeriya sun gaji da zaman gida

1 min read

Da alama ɗaliban Najeriya sun gaji da zama a gida bayan wata kusan huɗu da rufe makarantunsu a ƙasar da zummar ɗakile yaɗuwar annobar cutar korona.

Tun 26 ga watan Maris Gwamnatin Tarayya ta rufe dukkan makarantun ƙasar, matakin da ya shafi makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.

Sai dai a farkon watan Yuli gwamnati ta ce ɗaliban sakandare na shekarar ƙarshe za su koma azuzuwansu amma ba lallai ne hakan ta samu ba kasancewar gwamnatin ta ce ba za a rubuta jarrabawar WAEC ba ta 2020.

A ranar Juma’a matasan kasar suka kaddamar da maudu’in #SaveNigerianStudents wato “a ceci ɗaliban Najeriya” inda aka yi ta amfani da shi wajen bayyana abin da ke ransu fiye da sau 4,160 a shafin Twitter, inda da dama suke kira da a buɗe makarantun kamar yadda aka buɗe sauran harkoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *