July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Najeriya Na Sa Ran Samar Da Ayyuka 250,000 Ta Hanyar Hakar Gwal

1 min read

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis.

A cewar shugaban, yana fatan hakan ne sakamakon sauye sauyen da gwamnati ta yi kan dokokin hakar gwal a kasar.

“Sauye-sauyen sun bada kananan ‘yan kasuwa izinin hakar ma’adinai, wanda hakan zai bude wa kamfanoni hanyoyin sana’ar,” a cewar Buhari.

Hukumomi a Najeriya sun ce hakar ma’adinai ta haramtacciyar hanya, wacce aka fi yi a arewa maso gabashin kasar na taimakawa sosai wajen yawaitar aika-aikar ‘yan bindiga.

An kashe dubban mutane a yankin a cikin shekarun da suka gabata, duk da dai an jibge jami’an tsaro a yankin, ba a tsammanin tashin hankali a yankin zai kau nan ba da jimawa ba.

Buhari ya ce Najeriya ta rasa akalla biliyan 3 daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2018 saboda masu hakar gwal ba bira ka’ida ba.

Kudaden da gwal din zai samar wa Najeriya zai taimaka gaya yayin da cutar Coronavirus ke ci gaba da yin mummunar illa ga tattalin arzikin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *