June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

SarKin Zamfara ya Zargi wasu Mutane da taimakawa ‘Yan bindiga

1 min read

Sarkin Gusau a jihar Zamfara Alhaji Ibrahim Bello ya ce wasu daga cikin ‘yan jihar suna taimakawa ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane waje sayar musu da gidaje ko basu haya.
Sarkin na Gusau ya bayyana hakan ne lokacin da babban Sepeton ‘yan sanda na kasa, Muhammad Adamu Abubakar ya kai masa ziyara.
Alhaji Ibrahim Bello ya ce sun zauna da masu ruwa da tsaki a jihar domin kawo karshin matsalar da ake fusakanta ta ta’addaci a jihar sai dai abin yaci tura.
A cewar sa bayar da haya ga wasu al’umma jihar keyi, na taka rawa wajen yadda bata garin suke yin sojan gona suna shiga cikin jama’a suna aikata miyagun laifuka.
Alhaji Ibrahim Bello ya ce yan ta’addar na amfani da wannan damar ta zama a cikin al’umma suna kuma cin zarfin wadanda basuji ba basu gani ba,
Da yake jawabi a yayin ziyarar, babban Sefeton yan sandan kasar nan, Mohammad Adamu ya ce za suyi kokari wajen hada hannu da sauran jami’an tsaron kasar nan ganin an karkarde ayyukan bata gari a fadin kasar baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *