July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wajine Ministoci su girmama Majalisa

1 min read

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargaɗi ministoci da manyan jami’an hukumomin gwamnatinsa su kyautata alaƙa da majalisar tarayyar Najeriya.

Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkar yaɗa labaran shugaban, Garba Shehu ya fitar ta ambaton Buhari na cewa ba zai lamunci duk wani rashin mutunci ga majalisa daga duk wani jami’in ɓangaren zartarwa ba.

Ta ce shugaban ya yi wannan jan kunne ne lokacin da yake ganawa da shugabancin majalisun tarayya a jiya Alhamis, inda suka tattauna game da wasu ayyukan baya-bayan nan na majalisa.

Rahotanni sun ce jan kunnen na zuwa ne sa’o’i bayan shugaban hukumar raya yankin Neja Delta, Daniel Pondei ya fice daga zauren sauraron jin bahasi game da bincike kan harkokin kuɗin hukumar.W

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *