July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

za’a bude sauran filayen jiragen sama a Nigeria

1 min read

Gwamantin tarayya ta ce zata duba yiwuwar bude sauran filayen jiragen sama guda hudu dake jahohin kasar nan matukar za su yi biyayya ga dokokin da aka sharadanta na yaki cutar corona.
Karamin ministan harkokin sufurin jiragen saman kasar na Hadi Sirika ne ya bayyana hakan lokacin da yak e bayani ga baiwa kwamitin yaki da cutar corona na gwamnatin tarayya jiya a Abuja.
Hadi Sirika ya ce a yau juma’a ne ake sa ran kai ziyarar duba yiwuwar bude filayen jiragen da ke Calabar da Sokoto da Katsina da kuma jihar Kebbi.
Ya kara da cewa a ranar ashirin ga watan Yulin da muke ciki ne filayen jiragen za su ci gaba da gudanar da ayyukan su bisa tsarin da aka gindaya musu.
Hadi Sirika ya kuma ce kowanne filin jirgi zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa na yau da kullum karkashin ka’idoji da dokokin yaki da cutar corona kamar yadda hukumomin lafiya ke bada shawara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *