July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An sanya ranar komawa aiki

1 min read

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sanar da ranar
komawa aiki ga ma’aikata a fadin jihar baki daya.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta wallafa a shafinta na Twitter ta
ce ma’aikatan gwamnati a jihar da ke mataki na 14 za su koma bakin
aikinsu daga ranar Litinin 20 ga watan Yuli da muke ciki.
Sanarwar ta ce wajibi ne ga dukkan ma’aikatan su zama masu bin
dokar da mahukunta a bangaren kiwon lafiya suka shimfida.
Ta cikin sanarwar gwamnatin Kaduna ta ce masu mataki na 14 zuwa
sama za su rika zuwa aiki ne a ranakun Litinin da Laraba da kuma
Juma’a.
Amma daga masu mataki na bakwai har zuwa na 13 su za su koma
bakin aiki ne daga ranar Talata, kuma za su rika zuwa aiki sau biyu
ne kacal a sati a ranakun Talata da Alhamis daga karfe 9 na safe
zuwa uku na rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *