June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Katsina: Yadda abin fashewa ya kashe yara biyar a jihar

2 min read

‘Yan sanda a jihar Katsina sun fara bincike bayan wani abu da ake
zargin bam ne ya fashe a ƙauyen Yammama da ke ƙaramar
hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Mai magana da yawun ‘yan sanda reshen jihar Katsina Gambo Isah
ya tabbatar wa BBC da cewa yara biyar suka mutu sai kuma wasu
yaran shida suka raunata.
Da misalin ƙarfe 11:30 na safe, DPO na ‘yan sanda da ke Malumfashi
ya ce sun ji “ƙarar wani abu a gonar wani Alhaji Hussaini Mai Ƙwai”.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce, ” abin da ya fashewar ya
kashe yara biyar na wani mai suna Alhaji Adamu Yammama, kuma
yara shida da ke zaune a ƙarƙashin wata bishiya sun ji rauni’Yan sanda a jihar Katsina sun fara bincike bayan wani abu da ake
zargin bam ne ya fashe a ƙauyen Yammama da ke ƙaramar
hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Mai magana da yawun ‘yan sanda reshen jihar Katsina Gambo Isah
ya tabbatar wa BBC da cewa yara biyar suka mutu sai kuma wasu
yaran shida suka raunata.
Da misalin ƙarfe 11:30 na safe, DPO na ‘yan sanda da ke Malumfashi
ya ce sun ji “ƙarar wani abu a gonar wani Alhaji Hussaini Mai Ƙwai”.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce, ” abin da ya fashewar ya
kashe yara biyar na wani mai suna Alhaji Adamu Yammama, kuma
yara shida da ke zaune a ƙarƙashin wata bishiya sun ji rauni”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *