Matasa Kalilan ne zasu amfana da shirin Npower
1 min read
Masana na ci gaba da bayyana ra’ayoyin su kan kudirin Majalisar dokokin Jihar Kano,na ayyana hukuncin dandatsa a kan dukkan wanda aka kama da laifin aikata Fyade.
Wata Barrister a jihar Kano ta ce hukuncin dandatsa yayi tsauri domin kuwa idan aka fara dan datsa da yawa daga cikin ‘yan mat aka iya rasa samarin da zasu aura.
Inda ta ce daurin rai da rai shi ne mafi da cewa da dokar,inda ta ce akwai bukatar sake yin nazari a kan hukuncin ko kuma kudirin.
MUtane miliyan biyar ne suka ne shiga cikin shirin samar da aikin yi ga matasan Kasar nan karkashin shirin Npower.
A cewar Ministan Jinkai Sadiya Farouq ta ce ‘yan Kasar nan na cikin bukatar ayyukan yi,wanda hukuma hakanne ma gwamnatin Nigeria taga da cewar samarwa matasan wannan dama.
Hajiya Sadiya ta ce nan gaba kadan za’a biya ragowar matasan da suke bin gwamnati albashinsu wanda sun riga sun kammala ayyukansu,batare da an biya su kudaden ba.
Nigeria dai na fama da matasa da dama wanda suke zauna batare da samar da ayyukan yi ba,lamarin da ake ganin cewa shi ne ke kara ta azzara muggan laifuka a Kasar.