Matasa kalilan ne zasu amfana da shirin Npower
1 min readMutane miliyan biyar ne suka ne shiga cikin shirin samar da aikin yi ga matasan Kasar nan karkashin shirin Npower.
A cewar Ministan Jinkai Sadiya Farouq ta ce ‘yan Kasar nan na cikin bukatar ayyukan yi,wanda hukuma hakanne ma gwamnatin Nigeria taga da cewar samarwa matasan wannan dama.
Hajiya Sadiya ta ce nan gaba kadan za’a biya ragowar matasan da suke bin gwamnati albashinsu wanda sun riga sun kammala ayyukansu,batare da an biya su kudaden ba.
Nigeria dai na fama da matasa da dama wanda suke zauna batare da samar da ayyukan yi ba,lamarin da ake ganin cewa shi ne ke kara ta azzara muggan laifuka a Kasar.