September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Pogba zai sabunta zamansa a Manchester United, sai karshen Agusta Havertz zai koma Chelsea 17 Yuli 2020

2 min read

Dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, 27, yana dab da
amincewa da sabon kwantaragin shekara biyar a Manchester United.
(Sun)
Bayer Leverkusen ta amince da matakin da dan wasan Jamus Kai
Havertz, mai shekara 21, ya dauka na komawa Chelsea amma tana
so ta jinkirta tafiyarsa sai karshen watan Agusta. (Daily Star)
Manchester City na son dauko dan wasan Ajax da Argentina Nicolas
Tagliafico, mai shekara 27, a bazara. (Sports Illustrated)
Dan wasan Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29, yana da
kwarin gwiwar kammala tafiya Liverpool bayan ya ki amincewa ya
sabunta kwangilarsa a Bayern Munich. (Daily Mirror)
Manchester United ta kulla yarjejeniya da dan wasan Real Madrid
mai shekara 17 Alvaro Fernandez Carreras, wanda zai sanya hannu
kan kwangilar shekara hudu a Old Trafford. (AS – in Spanish)
Tsohon kocin Southampton da Tottenham Mauricio Pochettino na
cikin wadanda Inter Milan da Juventus suke son daukowa idan
kungiyoyin na Italiya suka kori koci-kocinsu – Antonio Conte da
Maurizio Sarri – a karshen kakar wasan bana. (Daily Telegraph)
An rage farashin Koulibaly, Man City na son ɗauko Martinez
Rashin kudin cefane na daga hankalin koci Arteta
Dole sai kocin Inter Conte ya gamsar da hukumar gudanarwar
kungiyar kafin a amince a kan albashin N’Golo Kante sannan a dauko
dan wasa na Faransa mai shekara 29 daga Chelsea. (SempreInter)
Dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, dan shekara 17, ya
kammala gwajin lafiyarsa a Borussia Dortmund gabanin tafiya
kungiyar daga Birmingham ko da yake zai kammala kakar wasan
bana a the Blues. (Sky Sports) .
Dan wasan Algeria Yasser Larouci, dan shekara 19, ya shirya barin
Liverpool a bazarar nan, inda aka ce Leeds da Brentford suna cikin
kungiyoyin da ke zawarcinsa. (Goal.com)
Watakila Tottenham za ta karasa kakar wasan bana ba tare da dan
wasan Ivory Coast Serge Aurier, mai shekara 27 ba, saboda ya tafi
Faransa sakamakon mutuwar dan uwansa. (Evening Standard)
Everton ta taya dan wasan Napoli Allan, amma kungiyar ta Italiya
tana jan kafa kan sayar da dan wasan na Brazil mai shekara 29.
(Sport Witness)
Roy Hodgson ya ce sayen sabbin ‘yan wasan da za su murza leda a
Crystal Palace a bazara zai bai wa kungiyar damar kara himma a
kakar wasan da ke tafe domin samun gurbin ‘yan goman saman
teburi. (Evening Standard)
Manchester City ta kulla yarjejeniya da dan wasan Valencia dan
kasar Sufaniya Ferran Torres, mai shekara 20. (Eurosport)
West Ham, Norwich da kuma Watford suna son dauko dan wasan
QPR dan kasar Jamhuriyar Ireland Ryan Manning, mai shekara 24.
(Football Insider) .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *