Shaguna da Tebura 300 hukumar Karota ta ruguje a daren jiya
1 min read
Knupda da Karota sun fara rusau a Kasuwar Sabon Gari.
Baya-bayan ne shugaban hukumar Karota ya bayyana cewa zasu fara ruguje tebura dake kasuwar wanda suke ba bisa ka’ida ba.
To sai dai kuma ‘yan kasuwar sun roki gwamnatin Kano data samar musu wani waje na daban,wanda zasu koma domin ci gaba da gudanar da kasuwancin nasu kamar yadda suka sa ba.
Ita ma hukumar tsara burane ta jihar Kano a wani sako data fitar ta umaeci dukkannin ‘yan kasuwar dake kantiti dasu kwashe kayan su cikin lumana.