July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan sanda sun kwato mata 10 daga hannun ‘yan bindiga

1 min read

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ceto wasu mata guda goma sha hudu wadanda ‘yan bindiga suka sace su sukayi garkuwa da su a daren jiya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Katsina SP Gambo Isah ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwar da ya fitar a yau asabar.

A cewar mai magana da yawun rundunar, a daren jiya ne ‘yan bindigar suka sace matan goma sha hudu a kauyen Kwantamawa da ke yankin karamar hukumar Dutsinma.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Katsina ya ce tun farko ‘yan bindigar wanda yawansu ya kai arba’in sun isa kauyen ne akan Babura dauke da bindigogi kirar AK47.

A cewar sanarwar ‘yan sandan sun ceto matan ne bayan musayar wuta da suka yi da ‘yan ta’addar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *