September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Cutar korona ta ƙara ɓulla a jihar Zamfara

2 min read

Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta sanar
da mai dauke da cutar korona na farko a Zamfara tun bayan sanar da
kawo karshenta a jihar.
Mutumin na cikin karin sabbin mutum 653 da hukumar ta snaar a daren
a sabar cewa suna dauke da wannan cuta.
Kamar yadda ta saba wallafawa a shafinta na tuwita ko wacce ranar
hukumar ta bayyana jihar zamfara da Cross River da Borno da Yobe a
matsyin jihohin da suka samu karin mutum duga a ranar Asabar.
Sai dai a gefe guda kuma, hukumomin lafiya a jihar ta Zamfara sun
nuna tababa kan wannan batu.
Yahaya Muhammad Kanomana shi ne kwamishinan lafiya na jihar, a
wata hira da ya yi da BBC ya ce wannan mutumi ba a Zamfara ya kamu
da wannan cuta ba zuwa ya yi da ita daga kasar Malesiya.
Ya ce mara lafiyar ne ya kai kansa ga jami’an lafiya na Zamfara domin
a yi masa gwaji, daga baya kuma aka tabbatar yana dauke da cutar.
“Ba mu killace shi ba, amma mun fara bibiyar wadanda ya yi mu’amala
da su, nan gaba za mu kai shi cibiyar killace marasa lafiya ta Yariman
Bakura.”
Zamfara ce dai jiha ta farko a Najeriya da ta bayyana kawo karshen
annobar korona a kasar, kafin daga bisani wasu jihohin da ba su fi biyu
ba suna su yi irin wannan ikirari.
Masu dauke da cutar korona a Najeriya yanzu sun kai 36,107 kuma
mutum sama da 14,000 sun warke yayin da 778 suka mutu sanadiyyar
wannan annoba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *