Kungiyar kW all on kafa ta Arsenal ta doke Manchester City 2-0
1 min read
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya yi wa mai gidansa Pep Guardiola zarra
yayin da ƙungiyarsa ta kai zagayen ƙarshe na Gasar cin Kofin FA da
nasarar da ta samu a Wembley.
Arteta, wanda ya bar aikinsa na mataimakin kocin Manchester City ya
je ya gaji Unai Emery a Arsenal cikin watan Disamba, yanzu dai ya
samu wata dama da zai iya yi wani abin a-zo-a-gani cikin kakarsa ta
farko.
Yanzu dai zai tafi cike da taƙama don fuskantar ƙungiyar Chelsea ko
Manchester United a karawar ƙarshe ranar 1 ga watan Agusta.
Gwarzon wasan Pierre-Emerick Aubameyang, zakaran duniya ɗan
gaban Arsenal na faɗi tashi don cimma sabuwar kwanturagi ta
dogon lokaci,, daidai lokacin da ya fito gazawar matakan baya na
Man city.
Aubameyang dai ya zunduma ƙwallo kai tsaye a ragar Ederson da
ƙwaƙƙwarar dama ɗaya da ya samu amma ƙaddara ta riga fata ga
City bayan minti na 19 lokacin da ya nuna gagarumar fasaha wajen
isar da ƙwallon da Nicolas Pepe ya kwaso.