April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Bukaci a Sake Nazari Kan Shekarun Daukar Aiki

2 min read

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ta 9, Ahmad
Ibrahim Lawal Photo: Ahmad Lawal Twitter (Twitter)
Majalisar Dattawan Najeriya ta
bukaci ma’aikatar kwadago da nagartar aiki ta kasar ta
kafa kwamitin da zai sake yin nazari akan tsarin
kayyade shekaru wajen daukar aiki, domin bai wa
matasa da suka kammala karatu damar samun ayyukan
yi.
Bukatar hakan na kunshe ne a cikin wani kudiri da dan
Majalisar Dattawa da ke wakiltar jihar Sokoto ta gabas
Sanata Ibrahim Gobri ya gabatar inda ya nemi a sake
yin nazari akan yadda hukumomin gwamnati da
kanfanoni masu zaman kansu suke kayyade shekaru na
daukar ma’aikata, wanda hakan ke sa da dama daga
cikin wadanda suke da takardun kammala karatu ba sa
samun guraben aiki.
Sakamakon karuwar rashin ayyukan yi a Najeriya, da
yawa daga cikin matasan da suka kammala karatun
digiri kuma suka shafe shekaru da dama suna neman
aiki, wasunsu sukan shiga aikata miyagun ayyuka da ke
hura wutar tabarbarewar sha’anin tsaro a kasar a
cewar Sanata Ibrahim Gobri.
Dakta Abdulhakeem Garba, na Kwalejin kimiya da
fasaha ta jihar Kaduna ya ce ana rasa kwarraru da za
su iya ba wa kasa gudunmowa sabili da shekarunsu sun
zarta yadda doka ta tanadar.
Sai dai a na shi bangaren Farfesa Shehu Abdullahi Zuru,
kuma masanin harkokin shari’a, ya ce zai yi wuya a iya
aiwatar da wannan kudiri duba da yadda ake sakaci da
dokoki a Najeriya.
Abun jira a gani shi ne ko kwalliya za ta biya kudin
sabulu, ganin cewa shugaban Majalisar Dokokin kasar
Ahmad Ibrahim Lawal ya yi na’am da kudirin kana ya
bukaci gwamnatin tarayya ta umarci ma’aikatar
kwadago da nagartar aiki akan ta kafa kwamitin da zai
sake yin nazari game da tsarin kayyade shekarun
daukar aiki cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *