July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mata Ne Suka Fi Fuskantar Tarin Matsaloli – Rahoton UNFPA

2 min read

Photo: VOA
A wani sabon rahoto da Asusun
kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya
UNFPA ya fitar, ya yi nazari akan halin da al’ummar
duniya ke ciki inda ya gano cewa mata ne suka fi
fuskantar tarin matsaloli, rahoton da aka yi wa take da
“Ba da son rai na ba,’’ lamarin da ke nuna rashin
daidaito tsakanin mata da maza na kara ta’azzara
ayyukan cin zarafi akan matan.
Irin wannan rahoto dai a duk shekara ake fidda shi don
duba halin da al’ummar duniya ke ciki, inda a bana
rahoton ya fi karkata akan halin da mata suka tsinci
kansu ciki musamman a wannan lokaci da dokar kulle
sakamakon annobar cutar COVID-19 ke dada kara
ayyukan cin zarafi ga mata kamar yadda Kori Habib,
wacce ke aiki da asusun kula da yawan jama’a na
Majalisar Dinkin Duniya a fannin hulda da ‘yan jarida a
Najeriya ta bayyana.
Ta ce akan tozarta ‘yaya mata ta hanyar hana su zuwa
makaranta, da auren dole, da auren wuri, ko hana
mace gado, fyade da sauransu, wadannan abubuwan su
suka fi ci wa Majalisar Dinkin Duniya tuwo a kwarya, a
cewarta.
Jami’ar lafiya a asibitin tarayya da ke Unguru a Jihar
Yobe, Hajja Muhammad, ta bayyana irin illolin da ke
tatttare da yi wa mata kaciya wanda hakan wani nau’i
ne na cin zarafin su.
Kwamishiniyar harkokin mata a jihar Nasarawa Hajiya
Halima Jabiru, ta ce wannan yanayi da duniya ta tsinci
kanta a ciki ya farkar da gwamnati musamman a
sha’anin da ya shafi kiwon lafiyar mata.
Wani babban kalubale da mata ke fuskanta a Najeriya
shi ne batun tabarbarewar sha’anin tsaro da ke
hargitsa musu rayuwar iyalinsu a cewar ‘yar fafutukar
kare hakkin mata Amina Yahaya.
Rahoton na Asusun kula da yawan jama’a a Majalisar
Dinkin Duniya na fatan za a kawo karshen jinkirin da
ake samu wajen aiwatar da dokar hana yi wa yara
mata auren wuri da yi musu kaciya da kuma yawan cin
zarafi ta hanyar lalata ko yi musu fyade da aka yi ta
samu a wannan shekarar ta 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *