June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan bindiga sun kashe sojoji a jihar Katsina

1 min read

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twiiter, ya ce yana da hotunan
irin mummunan kisan da aka yi wa sojojin.
A Najeriya dai ana yawan zargin sojojin ƙasar da taƙaita adadin
ɓarnar da ake yi musu, amma sau da dama sojojin kan musanta
wannan zargi.
Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke ci gaba da
cin karensu babu babbaka a arewacin Najeriya.
Rahotanni daga wasu ƙauyuka na jihar irin su Batsari da Dutsinma da
Jibiya da Faskari na cewa kaso mai yawa na manoman yankin ba su
yi sharar gona ba a wannan shekara ballantana niyyar fara noma
sakamakon matsi da suke fuskanta daga ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *