April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yaran da bam ya tashi da su ‘sun ɗauka kayan gwangwan ne.

1 min read

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta samu rahoton mutuwar yarinya ta
bakwai cikin yaran da wani abu da ake zargin bam ne ya tashi da su
cikin wata gona a ƙauyen ‘Yanmama na ƙaramar hukumar
Malumfashi.
Wani mataimaki na musamman ga gwamnan jihar, Muhammadu
Garba ya faɗa wa BBC cewa tashin farko yaro shida ne ya rasu, sai
wadda suka samu rahoton mutuwarta daga bisani.
“Za a kawo ta yanzu a haɗa su, su bakwai ke nan a yi musu jana’iza.
Akwai kusan aƙalla guda biyar da ke asibiti ana kula da su,” in ji shi.
Wannan ne dai karon farko da aka samu irin wannan al’amari na
tashin abin fashewa a jihar, mai fama da tarzomar ‘yan fashin daji,
abin da kuma ya tsananta fargabar da ake da ita kan ƙaruwar lamarin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce tuni aka tura ƙwararru kan
harkar abubuwa masu fashewa don gudanar da bincike game da
wannan al’amari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *