June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Geoffrey Onyeama: Buhari ya yi wa ministan da ya kamu da coronavirus addu’a

1 min read

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi wa Ministan harkokin wajen ƙasar Geoffrey Onyeama addu’ar samun sauƙi, bayan ya kamu da cutar korona.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar, shugaban ya bayyana Mista Geoffrey a matsayin wani babban ginshiƙi a mulkinsa, kuma ya yaba masa kan irin ƙoƙarin da yake yi wurin daƙile yaɗuwar korona.
Mista Onyeama dai na ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa domin yaƙar cutar korona.
A ranar Lahadi ne dai ministan ya bayyana cewa ya kamu da cutar korona
Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya ce an tabbatar da ya kamu da cutar bayan an yi masa gwajin cutar karo na huɗu.
A saƙon da ya wallafa, ministan ya ce a yanzu haka ya kama hanyarsa ta zuwa wurin killace masu ɗauke da cewar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *