April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kano: An yi garkuwa da ‘yar dan majalisa a jihar

1 min read

Wasu masu garkuwa da mutane sun sace ‘yar gidan ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ɗambatta, Alhaji Murtala Musa Kore da tsakar daren Asabar.
‘Yan bindigar sun ɗauki Juwairiyya ne da misalin ƙarfe 3:00 na dare bayan sun yi yunƙurin yin garkuwa da mahaifinta amma sai suka tarar ba ya nan, kamar yadda ɗan uwanta Jamilu ya shaida wa BBC.
Jamilu ya ce mahaifinsu yana birnin Kano a lokacin da ‘yan bindigar suka isa gidan nasu da ke ƙauyen Kore a Ƙaramar Hukumar Ɗambatta.
Juwairiyya Murtala Musa mai shekara 17, ɗaliba ce ‘yar aji biyar a makarantar sakandare ta Government Secondary School Jogana kuma ita ce ‘yar auta a wurin mahaifin nata.
“Mutum uku ne suka fara shigowa cikin gidan amma ba mu san yawan waɗanda suka tsaya a waje ba,” in ji Jamilu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *