June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rikici ya ɓarke tsakanin kwastan da al’ummar Jibia’

3 min read

Al’ummar Jibia da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya sun koka dangane da wani shinge da jami`an hukumar kwastan suka kafa a kusa da mashigar garin.
Mazauna garin da kewaye, musamman `yan kasuwa na zargin cewa jami`an hukumar na hana su shiga da kayan da ake samarwa na cikin gida, lamarin da ke jefa rayuwarsu a cikin kunci.
Sai dai hukumar a nata ɓangaren ta ce wasu na raɓewa da garin ne suna fasa-kwauri.
Ɗan majalisar da ke wakiltar al’ummar Jibia a zauren majalisar wakilan Najeriya, Sada Soli Jibia, ya shaida wa BBC cewa lamarin bai yi ɗaɗi ba saboda “yau a ce cikin ƙasa ba za a iya barin a kai simintin da ake yi a Najeriya ba ko gero ko dawa ko dusar da ake bai wa dabbobi ba za a iya kaiwa cikin kasa ba,”
“Wannan shi ne matsalar da muka samu da kwastan a Jibia, sun zo ƙofar shiga cikin gari, sun hana a kai irin waɗannan abubuwa kuma kowa yake da tarihin ƙasar Jibia, ya san muna da gagarumar kasuwa wadda tun da Kano daga Sokoto daga Kebbi daga Zamfara ake zuwa cin kasuwar nan,”
“Duk gidan biredin da yake Jibia yanzu, wanda suke yin biredi wanda duk yankunan ƙauyukanmu da suke zuwa nan suke hada-hada su siya, yau basu da damar da za su yi irin wadannan abubuwan domin yanzu biredi bai ma sayuwa a Jibia saboda an hana shigowa da fulawa.” in ji ɗan majalisar. Sada Soli Jibia ya buƙaci Shugaban hukumar ta kwastan Hameed Ali ya duba lamarin “kada ya zo wannan tsawwalawa da suka yi ya kawo wani halin da za a samu tashin hankali tsakanin mutanenmu da jami’an kwastan”.
Amma hukumar, ta bakin kakakinta Joseph Attah, ta ce sai da jami`anta na farin kaya ne suka gudanar da bincike suka gano wani ƙulli, sannan suka ɗauki matakin kafa shingen.
A cewar Attah “A kwanan nan, jami’an kwastan sun lura cewa kafin a gama kamar misali sati ɗaya sai a samu tireloli kusan 100 ko fiye da 100 su shiga garin Jibia, kuma abin da suke shiga da shi shi ne siminti, taki, dusa da kuma kayan gine-gine,”
Ya ce sun gano cewa sun ɗauki matakin hana tireloli shiga Jibia ne bayan da suka gano ana amfani da babura da suke ɗiban kayayyakin “su bi ta hanyar daji a yi fasa kwaurin waɗannan kayayyaki a fitar da su.” kamar yadda Joseph Attah ya bayyana.
“Duk wanda yake da shago kuma an tabbatar ga shagonka za a bar kayanka su shigo kuma su sauka a wajen.” a cewarsa.
Ba Jibia kadai ba, wasu al`umomin Najeriya mazauna kan iyaka da ke jihohin Zamfara da Sokoto, su ma suna irin wannan kuka na takurawa da suke cewa jami`an kwastan suna musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *