June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Bindiga Sun Kai Hare-hare a Karamar Hukumar Igabi a Kaduna

2 min read

‘Yan bindiga sama da dari ne su ka kai hari a garuruwan Kerawa, Rago, Zariyawa da Marina da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 3 suka kuma jikkata mutane 6, sannan suka sace dabbobi da kayan abinci.
Da misalin karfe tara na safiyar Lahadi 19 ga watan Yuli ne ‘yan bindigar kan babur, dauke da manyan makamai suka afkawa wadannan garuruwan kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa Muryar Amurka.
Hare-haren ‘yan bindiga a yankunan kananan hukumomin Birnin Gwari, da Igabi, da Giwa ya kara janyo fargaba ga manoma a daminar bana inji Alhaji Dayyabu Kerawa, wani mazaunin yankin.
Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta na daukar matakan sirri wajen magance matsalar tsaro a wadannan yankuna. Malam Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, ya ce a nan take bayan samun labarin abinda ya faru, aka tura jami’an tsaro wadannan yankunan, kuma sojojin kasa sun fattaki ‘yan bindigar, sannan na sama suka kai musu farmaki ta sama.
Ya kara da cewa a yanzu haka gwamnati da jami’an tsaro sun dauki matakin tsaro a wadannan yankunan.
Da ma dai jihar Kaduna na cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan-bindiga da kuma sace-sacen mutane don neman kudin fansa, ko a ranar Asabar din da ta gabata 18 ga watan Yuli sai da ‘yan bindiga suka sace wata ‘yar Sanda da diyarta, da kuma wasu mutum hudu a garin Janruwa da ke yankin Patrick Yakowa way a jihar ta Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *