July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An bude filin Jirgin sama a Kaduna

1 min read

A cikin wani rahoton jaridar The
Guardian, babbar daraktar sadarwa da hulda da jama’a
ta hukumar filayen jiragen saman Najeriya (FAAN),
Henrietta Yakubu, ta tabbatar da wannan ci gaban.
A cewarta filin jirgin saman Kaduna ma zai kasance a
sahun wadanda za’a bude a yau.
Filayen jiragen saman Margaret Ekpo da ke Calabar da
filin jirgin saman Yola a jihar Adamawa sun sake
budewa. A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta ce za ta
tabbatar da bin ka’idojin kariyar lafiya da tsaro, don
kauce wa rufe filayen jiragen saman da aka sake
budewa kwanan nan.
Ya zuwa yanzu, filayen jiragen saman 10 daga cikin 22
sun bude ayukan sufuri na cikin gida, a cikin
matsanancin yanayin rashin fasinjoji da yawan jiragen
da ke aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *