June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kashe mutum tara a wani sabon hari a Kaduna

1 min read

Rahotanni daga Jihar Kaduna a Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun sake
kai hari a kudancin jihar a daren Talata, inda aka kashe mutum tara.
Harin na zuwa ne ƙasa da sa’a 24 bayan kashe aƙalla mutum 18 aka
kuma jikkata wasu kimanin 30 yayin shagalin aure a ƙauyen Kukum-
Daji da ke Ƙaramar Hukumar Ƙaura.
Shugaban ƙungiyar al’umar kudancin Kaduna ta SOKAPU, Honourable
Jonathan Asake ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne
a ƙauyen Gora-Gan da ke Ƙaramar Hukumar Zangon-Kataf ranar Litinin
da dare, inda suka kashe aƙalla mutum tara.
Sai dai har zuwa yanzu ba mu kai ga jin ta bakin hukumomi a jihar ta
Kaduna ba. Muna fatan ji daga gare su nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *