June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Bazan cire manyan hafsoshin tsaran kasar nan iji Buhari

1 min read

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gwale ‘yan majalisar
dattawan kasar inda ya ki yarda da kiran da suka yi masa ya
sauke hafsoshin tsaron kasar.
A wata sanarwa da fadar shgaban kasar ta wallafa a shafinta na
Twitter, ta ce nadawa da sauke hafsoshin tsaron yana hannun
shugaban kasa don haka shi kadai ne zai yanke hukunci a kan
makomarsu.
“Ranar Talata, majalisar dattawa ta amince da da kudurin da ya yi
kira ga hafsoshin tsaro su sauka daga mukamansu ko kuma a
cire su saboda tabarbarewar tsaron kasar.
“Fadar shugaban kasa ta yi duba ga wannan kuduri, kuma tana
jaddada cewa nadawa da cire hafsoshin tsaro alhakin shugaban
kasa ne, kuma Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayinsa na
Kwamadan rundunar sojin Najeriya, zai yi abin da ya fi wa kasar
nan alfanu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *