June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumomi Sun Yi Kashedi A Kan Ambaliya A Kano Da Makwabtanta

2 min read

Itama hukumar kula da koramun
Hadejia da Jama’are ta ce ta yi tsare tsaren kubutar da
gonakin manoma daga wannan annoba a yankunan
jihohin Kano, Jigawa da kuma Bauchi.
Wani rahoto da hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta
fitar a makon jiya, ya yi hasashen cewa, jumlar
kananan hukumomi 102 ne daga cikin 774 na kasar, ka
iya fuskantar ambaliyar ruwa a damanar bana.
Rahoton ya nuna a jihar Kano, kananan hukumomi 17
ne cikin 44 na jihar zasu iya fuskantar ambaliyar.
Kadan daga ciki sune Gwarzo, Kura, Warawa Wudil ,
Rinmingado Nasarawa da kuma Kumbotso.
Dr. Kabiru Ibrahim Getso dake zaman kwamishinan
muhalli na jihar Kano ya ce rahotan na hukumar kula
da yanayi ta Najeriya ya zaburar dasu wajen daukar
matakan da suka dace.
Baya ga barazanar rusa muhalli, ambaliyar na lalata
amfanin gona na biliyoyin naira a kowace shekara,
al’amarin dake jefa manoma halin ni’yasu.
To amma hukumar kula da kogunan Hadejia da
Jama’are mai hurumi a sassan jihohin Kano Jigawa da
kuma Bauchi, ta ce ta dauki matakan da suka kamata
domin kubutar da manoman dake karkashin kulawar
ta.
Dinbin manoma ne dai ke tafka hasasara a kowace
shekara sanadiyar ambaliyar ruwa yayin da adadi mai
yawa na gine-gine ke rushewa a karkara da biranen
Najeriya a kowace shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *