July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar Dattawa ta bukaci a sauke hafsoshin tsaron Najeriya

1 min read

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi kira ga manyan hafsoshin tsaron
Najeriya su ajiye muƙamansu a daidai lokacin da ake ci gaba da
fuskantar matsalolin tsaro a ƙasar.
Sanata Ali Ndume ne ya gabatar da ƙudurin a lokacin zaman majalisar
na ranar Talata.
A cewar Sanata Ndume, ya gabatar da kudurin ne saboda irin yadda aka
yi wa sojoji kwanton-ɓauna a Katsina inda aka kashe da dama daga
cikinsu.
Sannan kuma ga wasu sojoji da suka yi murabus daga aiki.
A cewar Sanata Ndume waɗannan batutuwan biyu na da matukar tayar
da hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *