July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

MTN Na Shirin Bullo Da Wayar Zamani Maras Amfani Da Katin Sim

2 min read

Wannan sabuwar hanyar kawo
sauki a sadarwar zamani tana kunshe ne a wani mataki
na gaba da zai ba wadanda suke da manyan wayoyi
masu tsada su kai ga yin amfani da wayoyin su na
hannu ba tare da abin da ake kira sim kad ba, wanda
hakan yake nufin cewa za a iya amfani da layuka
dayawa a waya daya ta yin amfani da lamba kawai.
Jami’in kula da fanin Kimiya da Fasaha a Kamfanin
MTN Mohammed Auwal Abdullahi ya ce ilimi ne na
cigaba a kimiyance wanda kuma zai kawo sauki wajen
sadarwa da layuka iri daban daban a wayar hannu
guda kuma zai hana yawan sace sace da ake yi ta
hanyar amfani da sim kad.
A lokacin da yake bada bayanin wanan sabon salo,
Injiniya Bako Wakil wanda shi ne mai kula da fanin
Inganci da Nagarta na Hukumar Kula da Hanyoyin
Sadarwa ta kasa, ya ce hukumar ta bada izinin a yi
wanan gwaji na tsawon shekara daya domin a ga yadda
zai taimaka wajen bunkasa hanyar sadarwar ba tare da
yawan matsalolin da ake samu ba irin su sace sacen
kudadaen mutane a banki da sace mutane a yi garkuwa
da su da kuma sace wayoyi masu dauke da bayanan
sirri na manyan jami’ai.
Ya ce wanan sabuwar hanaya za ta bada dama mutum
ya yi mu’amala da mutane a ko ina suke a duniya ta
yin amfani da lamba daya kawai.
Abin jira a gani shi ne ko wanan sabon salo zai kai ga
kawo wa talaka sauki wajen sada zumunta da cutar
Korona Bairus ta takaita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *