April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutane 229 suka mutu

1 min read

Iran ta bayar da rahoton mutuwar mutum 229 a cikin awa 24 da suka
gabata sakamakon cutar korona – adadi mafi yawa kenan tun bayan
ɓarkewar cutar a ƙasar.
Sima Sadat Lari, mai magana da yawun Ma’aikatar Lafiya ta ce jumillar
adadin waɗanda suka mutun sun kai 14,634 da kuma 278,827 da suka
harbu da ita a Iran.
Ƙasar ta funskanci ƙaruwar masu kamuwa da cutar tun bayan da ta
sassauta dokokin kulle a tsakiyar watan Afrilu domin farfaɗo da tattalin
arzikinta, wanda dama yake fama da takunkumin da Amurika ta ƙaƙaba
masa.
Shugaba Hassan Rouhani ya faɗa a farkon watan nan cewa Iran ba za
ta iya sake rufe harkokin kasuwancinta ba kuma ya shawarci Iraniyawa
da su saka takunkumi da kauce wa cunkoson jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *