July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaban Nigeria Buhari ya kadu game mutuwar Isma’il Isah Funtuah

1 min read

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana kaɗuwarsa kan
rasuwar amininsa Malam Isma’ila Isa Funtua wanda ya rasu ranar
Litinin.
Shugaban ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwa da kuma
al’ummar Jihar Katsina da ma sauran makusantan marigayin bisa
rasuwarsa.
Shugaba Buhari cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai ba shi
shawara kan kafafen yaɗa labarai ya fitar ya bayyana marigayin a
matsayin “mutum na kowa da ake matuƙar girmamawa.”
Fadar shugaban ba ta yi wani cikakken bayani ba game da dalilin
rasuwarsa amma an ruwaito makusantansa na cewa ya rasu ne
sanadiyar bugun zuciya.
Malam Isma’ila Isa Funtua yana cikin manyan wadanda ake ganin
suna da tasiri a gwamnatin Buhari.
Kuma tsakanin wata uku dai yanzu shugaban ya rasa manyan
aminansa guda biyu bayan rasuwar Abba Kyari shugaban ma’aikatan
fadarsa da ya rasu watan Afrilu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *