July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan bindiga sun kashe mutum 18 a gidan biki a Kaduna

2 min read

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga
sun kashe akalla mutum 18 da kuma jikkata wasu 30 a gidan biki.
An kai harin ne a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna kan masu
bikin aure a kauyen Kukun-Daji.
Lamarin dai ya faru ne a jiya Lahadi da tsakar dare. Bayanai na cewa
ango da amaryar da ake bikinsu, sun tsira daga harin.
Wani shugaban al’umma daga yankin Kaura, Jonathan Asake ya
shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun bude wuta ne yayin da
mutane ke ta cashewa, sannan daga bisani suka tsere.
Jonathan ya ce nan take mutum 15 suka mutu – sauran uku kuma
sun mutu ne a asibiti lokacin da ake ba su kulawar gaggawa. Kakakin ‘yan sanda a jihar ta Kaduna, Muhammad Jalige ya tabbatar
wa BBC da kai harin, amma bai yi karin haske kan adadin mutane da
aka kashe ba.
Sai dai yana mai cewa hukumomi na tattara bayanai, ya kuma kara
da cewa suna iya kokarinsu don tabbatar da tsaro a jihar.
An sha kai irin wannan muggan hare-hare a kan babura a jihohi da
dama da ke arewa maso yammacin Najeriya, tare da kashe ko sace
mutane don neman kudin fansa wani lokaci a kwashe musu dukiyoyi.
A ranar Asabar ma, an kashe akalla jami’an tsaro 16 ciki har da
manyan hafsoshi uku yayin da suka yi kokarin kutsawa cikin wani
daji da ‘yan fashi ke mafaka a jihar Katsina.
Sojojin Najeriya sun ce sun yi nasarar kashe mutum 17 daga cikin
‘yan fashin a lokacin musayar wuta.
Sama da mutum dubu takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon
irin wadanan hare-hare a cikin shekaru 10 a yankin arewa mao
yammacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *