July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za’a bude Makarantun Allo dana Islamiyya a Kano

1 min read

Hukumar kula da makarantun Alqur’ani da Islamiyya ta Jihar ta bukaci Malaman Makarantun islamiyya da dalibansu dasu Kara hakuri,dan kuwa gwamnati na cigaba da shirin bude Makarantun baki daya.

Shugaban hukumar Sheikh Gwani Yahuza Gwani Dan zarga ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema labarai a hukumar dake nan Kano.

Sheikh Gwani Yahuza ya kuma ce gwamnatin Jihar Kano ta damu matuka da yadda daliban ke zaune a gidajensu tare da komawa makarantun bako dana Islamiyya ba.

Shugaban Kara da cewa akwai makarantun da suka Samu labarin sun bude amma saboda gudun Jan magana yasa basu dauki mataki akansu ba,amma akwai bukatar malaman su ringa kiyaye doka.

Ya kuma Kara da cewa annoba All..yayi umarnin cewa duk lokacin da annoba ta bayyana wajibine abi matakan kare al’imma daga hatsarinta.

Jaridar Bustandaily ta ruwaito cewa Shugaban hukumar na cewa Gwamnati ta kusa gama tattaunawa da Jami’an lafiya kan bude Makarantun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *