April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Abin takaicine ganin yadda ‘yan bindiga ke cin karansu babu babbaka

1 min read

Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana damuwa da takaici dangane
da yawaitar hare-hare da kashe-kashen mutane a arewacin ƙasar.
A cewar majalisar, zai yi wuya a shawo kan matsalolin tsaro da ke
addabar ƙasar, idan ba a wadata sojoji da kayan yaki na zamani ba.
Senata Muhammad Ali Ndume shi ne ya gabatar da ƙudirin neman
manyan hafsoshin tsaron Najeriya su ajiye muƙamansu saboda
yadda ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a ƙasar.
A cewarsa, “cikin sati biyu ko uku da suka wuce, Najeriya ta rasa
sojoji fiye da 40, wannan ba ƙaramin abu ba ne”.
A ganinsa, akwai buƙatar a matsawa gwamnati lamba domin ta
inganta aikin sojoji ta hanyar samar da ƙarin sojojin da kuma kayan
aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *