July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kama ‘yan fashi da makami 15 a jiya.

1 min read

Rundinar ‘yan sandan jihar Jigawa ta sami nasarar damke wasu gungun ‘yan fashi, dake bin mutane har gida da makamai suna kwace musu kudi da kuma dukiya.
Rundunar ta ce, ta samu kira daga kauyen Yargaba dake yankin karamar hukumar Dutse ranar 15 ga watan Yulin da muke ciki, inda aka sanar dasu cewa, wasu ‘yan fashi dauke da muggan makamai sun shiga kauyen cikin dare, suna kwacewa mutane kayan da suka mallaka.
Sai dai da zuwan ‘yan sanda, sai suka tarar ‘yan fashin sun tsere, sai dai binciken ‘yan sanda ya samu nasarar kamo matasa 7, ‘yan kungiya daya, wadanda bincike ya nuna, su ne ke addabar mutane a Dutse da sauran sassa, wajen aikata fashi da makami.
Daya daga cikin wadanda ake zargi Isah Ali Dawa Soja wanda ya amsa cewa shine jagoransu, an same shi da kakin sojoji, da kuma bindiga kirar fiston a gidan sa, ya yin da jami’an ‘yan sandan ke gudanar da bincike.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa SP. Abdu Jinjiri a wata sanarwa da da ya aikewa manema labarai a yammacin jiya.

Ya Kara da cewa, su na ci gaba da bincike, don gano sauran wadan suka gudu, da kuma irin makaman da suke amfani dashi a kauyuka suna aikata fashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *