June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An sami matsala a wasu asbitoci

1 min read

Asibitoci a Madagascar sun shiga wani hali bayan ƙara yaɗuwar cutar
korona a ƙasar.
A baya dai shugaban ƙasar ya ta tallata wani jiƙo na tazargade a
matsayin maganin na korona.
An sake samun mutum 614 da suka kamu da cutar ta korona a ƙasar
wanda a halin yanzu adadin waɗanda suka kamu da cutar ya kai 8,162
sai kuma mutum 69 da aka tabbatar da sun mutu.
Tuni ƙasashen Afrika bakwai suka bayar oda domin kawo musu
tazargaden na Madagascar.
Sai dai Hukumatr Lafiya Ta Duniya ta bayyana cewa babu wani tabbaci
da ke nuna cewa tazargaden na Madagascar na magance cutar ta
korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *