July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ba’a bude masallacin harami ba

2 min read

Manjo Janar Mohammed Bin Wasl Al-Ahmadi, mataimakin shugaban
jami’an tsaro na Masallacin Harami yayin aikin Hajji, ya faɗa ranar
Talata cewa masallacin zai ci gaba da kasancewa a rufe a ranakun
Arafa da Idin Babbar Sallah saboda hana bazuwar cutar korona.
Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruewaito shi yana
cewa: Dakatar da sallah a cikin masallacin da harabarsa zai ci gaba da
aiki. Mun shawarci mutanen garin Makkah da su karya azuminsu na
Ranar Arfa a gaidajensu,” in ji shi.Manjo Janar Al-Ahmadi ya yi
wadannan jawabai ne a yayin wani taron manema labarai inda ya sanar
da kammala matakin farko na tsara Aikin Hajjin bana.
Ya ce tsarin tsaro na hajjin bana zai mayar da hankali ne kan tsaro da
jin kai da batun lafiya.Mun mayar da hankali ne bana kan batun lafiya
saboda yanayin da aka samu kai a ciki. Sauran matakan za a kammala
su a kwanaki masu zuwa,” in ji Manji Janar Al-Ahmadi.Ya ce an sanya
sabon tsari don lura da shiga da fitar mahajjata cikin Masallacin
Haramin don tabbatar da cewa an bi dokar yin nesa-nesa da juna.Daga
cikin matakan kariyar da aka dauka, an kebe hanyar zuwa wajen dawafi
da na Safa da Marwa, sannan za a bar masu izini a hukumance su
shiga harabar masallain in ji Manjo Janar Al-Ahmadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *