Dan Sanda ya mari ma’aikaciyar jirgin sama
1 min read
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama a Najeriya ta zargi shugaban
‘yan sandan DSS da cin zarafin wani ma’aikacin hukumar a filin jirgin
sama na Abuja.
Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN) Safiyanu Abba, shugaban
DSS na filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, ya mari wani ma’aikacin
hukumar saboda ya ankarar da shi bayan ya karya dokar hukumar.
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a 17 ga watan Yuli, in ji hukumar,
sannan Safiyanu ya sake karya dokar tsaro ta filin jirgin saboda ya
bayar da umarnin a lalube wani matafiyi.
BBC ba ta ji ta bakin Safiyanu Abba ba game da lamarin amma
hukumar ta ce ta kai ƙararsa, duk da cewa ba ta bayyana inda ta kai
ƙarar ba.
“Hukumar FAAN ta yi Allah-wadai da wannan ɗabi’a ta karya doka da
kawo cikas ga tsarin tsaro a filin jirgin,” in ji hukumar a wani saƙon
Twitter da ta wallafa.