September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Katsina: Ƴan bindiga sun sace mata 17

2 min read

Al’ummar garin Zakka a jihar Katsina sun ce wasu ‘yan bindiga da ba
su san ko su waye ba sun kai masu hari inda suka sace mata 17 da
kuma kwashe shanu da dukiyoyinsu.
Wani mazauni garin na Zakka da ke cikin ƙaramar hukumar Safana
ya shaida wa BBC cewa ƴan bindigar sun shiga garin ne tsakar daren
Lahadi inda suka shafe sama da sa’a biyu suna fashi.
Ya ce ƴan bindigar sun shigo garin ne misalin karfe 12 na dare kuma
suka f ara harbin bindiga wanda ya razana mutanen garin wasu suka
ruga daji wasu kuma suka boye a cikin karan dawa da gero.
“Sun kwashe shanu da dama da tumaki sannan suka shiga gida gida
suna kwatar dukiyar mutane kafin su tafi da mata da ‘yan mata 17,”
inji shi.
Amma ya ce ɓarayin sun mayar da wata yarinya ƴar wata byar da
haihuwa da kuma hudu daga cikin matan da suka ɗauka da ya ce
suma Allah ya kuɓutar da su.
Ƴan bindigar dai ba. Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke ci gaba da
cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotanni daga wasu ƙauyuka na jihar irin su Batsari da Dutsinma da
Jibiya da Faskari na cewa kaso mai yawa na manoman yankin ba su
yi sharar gona ba a wannan shekara ballantana niyyar fara noma
sakamakon matsi da suke fuskanta daga ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *