June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotu ta bada yan sanda umarnin kama shugaban Hisba tare da kwamishinan Shari’a

1 min read

Wata kotun shara’ar musulunci dake zama a karamar hukumar Tudun Wada a jihar Sokoto ta bada umarnin kama kwamandan rundunar Hizbah Dakta Adamu Bello Kasarawa da wasu manyan jami’an hukumar ta jihar kan bijirewa umarnin kotun na kin amsa gayyatarta.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da kotun ta bayar bayan da wata mata masi suna Hadiza Abubakar ta shigar da kara gaban kotun tana zargin shugaban rundunar Hizban ta Jihar Sokoto da mallakawa tsohon mijinta Habibub Bawa dansu dan shekara biyu kacal wanda hakan k,uma ya sabarwa shariar musulunci.
Da aka tuntubeshi kwamandan rundunar Hizban ta tabbatar da umarnin da kotun ta bayar saidai sun mika lamarin ga bangaran shara’a na hukumar don basu shawarwari kan almarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *