July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ni kadai ke da hurumin sauke hafsoshin tsaro-Buhari

1 min read

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce shi kadai ke
da hurumin nadawa ko sauke wani babban hafsan soji a
mukaminsa, sabanin umurnin da Majalisar Dattawan
kasar ta bayar da ke cewa, hafsoshin sojin su sauka ko
kuma a sauke su daga mukamansu. Sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Femi
Adeshina ya rattaba wa hannu ta ce, shugaban ya ji matsayin da
Majalisar Dattawan ta dauka a wannan Talatar, amma su san da
sanin cewar, babu wanda yake da hurumin nada hafsan soji ko kuma
sauke shi daga mukaminsa sai shi kadai.
Ita dai Majalisar Dattawa ta tafka mahawara kan tabarbarewar tsaro
da kuma kashe sojojin kasar da ‘yan bindiga suka yi a Jihar Katsina,
inda ‘yan majalisun suka nuna rashin amincewarsu da tabarbarewar
al’amura a cikin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *