June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Nigeria zata fara siyan manfetir a Nijar

2 min read

An ƙulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kamfanin man fetur na
najeriya, NNPC, da kuma na Nijar, SONIDEP, game da sayar wa
Najeriya tataccen mai da za ta riƙa amfani da shi a cikin gida.
Ba wannan ce yarjejeniyar farko da kasashen biyu suka ƙulla ba kan
wannan batu sai dai wannan ne karon farko da za su ɗauki ƙwararan
matakai don ganin yarjejeniyar ta yi nasara.
An dakatar da waccen yarjejeniya ne tun bayan da hukumomin Najeriya
suka ɗauki matakin rufe iyakokin ƙasar, abin da ya jawo dakatar da
shiga da man ƙasar.
Ita ma annobar korona ta ƙara tillasata wa kasashen ɗaukar matakan
ba-sani-ba-sabo.
Nijeriya ta ce sayen man daga Nijar zai rage mata wasu wahalhalu da
take fuskanta wajen sawo man da take amfani da shi cikin gida daga
ƙasashen Turai.
A watan Nuwamban 2011 ne Nijar ta shiga sahun ƙsaashen da ke haƙo
man fetur.
Kampanin NCCC na China ne gwamnatin ƙasar ta damka wa alhakin
haƙo man daga Agadem na Jihar Diffa tare da tace shi a garin Ɗan
Baki na Jihar Damagaram, yayin da kamfanin mai na ƙasar, SONIDEP,
ke da alhakin kasuwancinsa.
Kampanin da ke tace man futur a Nijar, SORAZ, na tace gangar mai
20,000 a kowace rana, wanda shi ne za a fara sayar wa Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *