September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ranar Juma’a za’ayi Sallah a Nigeria

1 min read

Ranar Juma’a za a yi Babbar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi
Kwamitin ganin wata da ke karkashin shugabancin Sarkin Musulmi na Najeriya ya ce ranar Juma’a 31 ga watan Yuli za a gudanar da Idin Babbar Sallah.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kamitin ya ce an ga sabon watan Dhul Hijjah a wurare da dama ma kasar ranar Talata, don haka yau Laraba ce daya daga watan Dhul Hijjah.

A cewarsa, an ga sabon watan ne a Abuja da Jalingo da Ilorin da Lafiya da Minna da kuma Misau.

Ya kara da cewa masarauta Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III za ta fitar da sanarwa a hukumance da za ta yi cikakken bayani kan tsarin Babbar Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *