April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaba Buhari zai tafi ƙasar Mali

2 min read

Tafiyar ta shugaban ƙasar ta biyo bayan tattaunawarsa da Tsohon
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu
shiga tsakani daga ƙunigyar ECOWAS da suka je Mali domin kawo
sasanci.
Wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika irin su
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sun amince su hadu a Mali
domin tattaunawa don kawo sasanci tsakanin Shugaban Mali
Boubacar Keita da kuma ‘yan adawa a ƙasar.
Ana sa ran Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da kuma na Cote
d’Ivoire Alassane Ouattara za su halarci tattaunawar.
Wannan ne karo na farko da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
zai fita Najeriya tun bayan da aka kulle iyakokin ƙasar sakamakon
annobar cutar korona.
A baya dai ‘yan ƙasar na yawan ƙorafi dangane da tafiye tafiyen
shugaban ƙasar. A ranar Litinin ne tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya
kai wa Shugaba Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja, inda suka
tattauna a wata ganawar sirri.
Saƙon Twitter da Buhari ya wallafa ya nuna cewa Jonathan ya je
Fadar Aso Rock Villa domin miƙa rahoton aikin sasanta rikicin siyasa
ne wanda ƙungiyar ECOWAS ta tura shi ƙasar Mali a makon da ya
gabata ga Buhari.
“Na karɓi rahoton wakilin ECOWAS na musamman a Mali, tsohon
Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, game da rikicin siyasar Mali
kuma za mu nemi shugaban ƙungiyar, Shugaban Nijar, ya yi mana
cikakken bayani a matsayinsa na shugaba,” in ji Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *