June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojoji sun kashe mayaka bakwai

1 min read

Sojojin Amurka sun bayyana cewa sun kashe masu mayaƙan ƙungiyar
IS bakwai a arewa maso gabashin Somalia.
Rundunar sojojin Amurka da ke aiki a Afrika ta bayyana cewa sojojin
Amurka tare da hadin gwiwar na Somalia sun kai harin ta sama ga ‘yan
ƙungiyar ISIS-Somalia bayan wani hari da suka kai ga sojojin kusa da
ƙauyen Timirshe.
Sojojin Amurkan sun bayyana cewa ba a raunata wani farar hula ba ko
kuma kisa yayin harin.
Wani gidan Rediyo a Somalia ya ruwaito cewa sojojin sa kai na yankin
sun kashe mayaƙan IS 20.
Ƙungiyar ta IS na ci gaba da kai hare-hare a ƙasar kusan shekaru biyar,
sai dai ƙungiyar al-Shabab na neman shafe ƙungiyar ta IS.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *