July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan bindiga sun sace mutane hudu

1 min read

‘Yan bindiga sun sace wasu ‘yan China hudu masu aikin gine-gine a
jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.
Kwamishinar ‘yan sanda ta jihar, Irene Ugboh Itohan ya tabbatar wa
BBC faruwar lamarin.
Ta ce an kashe wani dan sanda da ke aiki da ‘yan Chinan a lokacin
sace su ɗin a yankin Akampka a ranar Talata da daddare.
An tura jami’an tsaro wajen don neman ‘yan Chinan.
Har yanzu ba a san dalilin sace su din ba, amma satar mutane don
karɓar kudin fansa abu ne da ya zama ruwan dare a fadin Najeriya,
sannan abin bai bar kan kowa ba baƙi da ‘yan kasa.
A wasu lokutan masu satar mutanen kan kashe waɗanda suka sace
idan har ba a biya kuɗin fansa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *