Yar Dan majalisa wacce masu garkuwa da mutane ta kubuta
1 min read
Yar dan majalisa mai wakiltar danbatta da masu garkuwa suka sace ta shaki iskar yanci.
Juwairiyya Murtala ‘yar ‘dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar karamar hukumar Danbatta Murtala Musa Kore da aka sace.
Jaridar intanet ta Kano Focus ta rawaito cewar, Juwairiyya ta dawo gida, garin Kore na karamar hukumar Danbatta da karfe misalin 3:30 na daren Talata.
Nura Yusha’u Kore wanda ‘dan uwa ne a gare ta shi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce ta dawo gida cikin koshin lafiya.
A ranar Asabar da ta gabata ne, wasu masu garkuwa da mutane su kayi awon gaba da Juwairiyya mai shekaru 17 a duniya.
Sai dai har zuwa wannan lokaci hukumomin tsaro a Kano ba su ce komai ba game da sace ta dama dawowar ta gida.